in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwwa da kasar Sin ya sassauta cututtuka a nahiyar Afrika
2016-02-02 11:26:25 cri
Hadin gwiwwa a bangaren kiwon lafiya ya taimaka sosai wajen sassauta samun cututtuka a nahiyar Afrika sanna ya karfafa karfin kai dauki cikin sauri ga sabbin cututtukan dake bulluwa,inji wani babban jami'I a kungiyar tarayyar kasashen Afrika.

Mustapha Sidiki Kaloko Kwamishin walwalar jama'a na kungiyar AU a hirar da yayi da Xinhua a lokacin taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ta AU yace kasar Sin ta bada gudunmuwa sosai wajen samar da kayayyakin kiwon lafiya na zamani a nahiyar.

Mr Kaloko yace sawun Sin a bangaren kiwon lafiya na kasashen Afrika ya fadada ya kaiwa a fannoni kamar binciken cututtuka da bada horo ma jami'an kiwon lafiya da kuma samar da kayayyakin aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na karkara.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a cikin jawabin da yayi a taron kolin dandalin hadin gwiwwa tsakanin Sin da Africa wato FOCAC da aka yi a watan disambar bara a Johannesburg na kasar Afrika ta kudu yace Beijing zata karfafa hadin gwiwwa a bangaren kiwon lafiya da kasashen Afrika.

Kwamishinan walwalar jama'ar na AU yace kasashen Afrikan su ma a shirye suke su hada hannu da kasar Sin domin taimakawa wajen dakile cututtukan da aka iya dauka kamar malariya da tarin fuka da kuma sida da ma sauran cututtuka da aka yi watsi da su kamar Kalaazar, trachoma da ciwon barci.

Ya lura da cewar kasar Sin na kan gaba cikin kasashen da suka fara kai dauki cikin gaggawa bayan barkewar cutar Ebola a kasashen Liberiya, Saliyo da Guinea.

Har ila yau Mr Sadiko ya ce ma'aikatan jinya na kasar Sin sun hada cibiyar binciken cututtuka tun kafin ma a samu barkewar cutar Ebola ya kai wani mizani.

Ya tabbatar da cewar akwai isassun magungunan bada kariya don gudun sake barkewar wata annobar ta Ebola a Afrikan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China