Masana a harkar lafiya da ke wani taro a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda sun yi kiran da a kara gudanar da bincike game da cutar mura a Afirka, da nufin fito da matakan da suka dace na magance wannan matsala da ta addabi jama'a.
A jawabinta na bude taron da za a shafe kwanaki 3 ana gudanar da shi, ministar kiwon lafiya ta kasar Rwanda, Agnes Binagwaho, ta ce, cutar mura, cuta ce da ta shafi jama'a baki daya, don haka hallara jama'a zai taimaka a sauran fannoni na kiwon lafiya. Har ma ta ba da misali da yadda aka yi wa cutar Ebola taron dangi wajen yakar ta.
Manufar taron game da magance cutar ta mura a nahiyar ta Afirka ita ce karfafa gwiwar gudanar da bincike kan cutar ta mura a Afirka, saukaka hanyoyin samun alluran rigakafi, musayar bayanai, dabaru da kayayyakin aiki da nufin tunkarar cutar.
Sama da masana harkar lafiya 150 daga sassa daban-daban na duniya ne ke halartar taron na Kigali, wanda shi ne karo na 5 a jerin tarukan da masanan ke shiryawa.(Ibrahim)