in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya murnar bikin wake-wake da raye-rayen matasan Asiya da Afirka karo na farko
2016-07-28 13:26:59 cri

Yau Alhamis, an kaddamar da bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a nan birnin Beijing, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasika domin taya murnar bikin, inda ya nuna alheri cewa, za a gudanar da bikin cikin cikakkiyar nasara.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasashen Asiya da Afirka suna da yawan matasa a fadin duniya, kuma matasan suna taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen nahiyoyin biyu, da kuma kiyaye zaman lafiya a fadin duniya.

Kazalika, shugaba Xi ya sa ran cewa, matasan Asiya da Afirka za su ci gaba da aiwatar da ka'idoji goma da aka tsara a yayin taron da kasashen Asiya da Afirka suka yi a birnin Bandung na kasar Indonesiya a shekarar 1955, domin kara karfafa cudanya da fahimtar juna da hadin gwiwa dake tsakaninsu, kana shugaba Xi yana fatan matasan za su kara yin kokari matuka domin ciyar da tattalin arzikin Asiya da Afirka gaba yadda ya kamara, tare kuma da amfanawa jama'ar Asiya da Afirka da kuma fadin duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China