Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, kuma ya yi jawabi, inda ya jaddada cewa, dole ne a sanya aikin kiwon lafiyar jama'a a matsayin muhimman al'amari da za a kara mai da hankali wajen bunkasa shi cikin dogon lokaci, ta yadda za a iya tabbatar da ganin an kiyaye lafiyar jama'ar kasar Sin daga dukkan fannoni, a kowane lokaci a yi kokarin gina wani kakkarfan tushe don cimma burin kasar Sin na sake farfadowar al'ummarta a lokacin da ake murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2021, da taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 2049.
Bugu da kari Xi Jinping ya jaddada cewa, a cikin dogon lokacin da ya gabata, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen nune-nunen wata babbar kasa wadda take kokarin sauke nauyin da ya wajaba a kanta na kasa da kasa na kokarin ba da jinya a duk fadin duniya, sakamakon haka, ta samu yabo sosai daga gamayyar kasa da kasa.
Shugaba Xi, ya nemi a kyautata ayyukan kula da lafiya ta gaggawa domin tinkarar al'amuran kiwon lafiya na ibtila'i da ka iya faruwa a sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen)