Koda yake yanzu ana gudanar da aikin neman mutane da sauran ayyukan ceto, sai dai kasancewar girgizar kasar ta auku ne da daddare, gine gine sun danne mutane da yawa a gidajen su yayin da suke yin barci, kana babu hanyoyin motoci masu kyau a garin Amatrice dake yankin Appennino. Ana dai hasashen cewa, yawan mutanen da suka mutu ko raunata a sakamakon girgizar kasar zai karu.
A safiyar ranar Laraba ne masu bada ceto daga yankuna da kewaye suka isa wurin, kana yanzu sojoji da 'yan sanda sun shiga ayyukan ceton, kuma masu aikin sa kai daga wurare daban daban sun isa wurin don bada taimako. (Zainab)