A jiya, shugaban kasar Rafael Correa Delgado ya yi rangadi a yankuna masu kusa da teku da bala'in ya fi shafa ta cikin jirgin sama mai saukar ungulu, inda ya furta cewa, girgizar kasar ta haifar na barna mai tsanani, yayin da wasu mutane da yawa suke karkashin buraguzan gine gine. Shi ya sa mai yiwuwa ne yawan mutuwar mutane zai ci gaba da karuwa.
A garin Pedernales dake tsakiyar yankin da girgizar kasar ta faru, an tsugunar da masu fama da bala'in sama da dari daya a rumfunan da aka kafa a wani filin wasan kwallon kafa.
Ma'aikatar harkokin wajen Ecuador ta bayyana cewa, kasashen Bolivia, Switzerland, Spain da sauransu sun tura masu aikin ceto zuwa kasar bi da bi, yayin da aka kebe kayayyakin agajin jin kai zuwa kasar a kai a kai.(Fatima)