in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya aika da sakon jajantawa ga takwaransa na kasar Ecuador game da bala'in girgizar kasa
2016-04-19 09:53:17 cri

A jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon jajantawa ga takwaransa na kasar Ecuador Rafael Correa Delgado wadda ke fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani.

Inda Xi Jinping ya bayyana cewa, girgizar kasar mai tsanani da ta faru a kasar Ecuador ta ba shi mamaki sosai, wacce ta haddasa hasarar rayukan mutane da dukiya mai yawa. A madadin gwamnatin kasar Sin da kuma jama'arta, ya mika ta'aziyya ga mutanen da suka mutu, kuma tana jajantawa iyalansu. Sanna shugaba Xi ya yi imanin cewa, a karkashin shugaba da gwamnatin kasar Ecuador, jama'ar kasar za su iya cimma nasarar yaki da bala'in da kuma farfado da zaman rayuwarsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China