in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi girgizar kasa mai karfin 6.8 a kasar Myanmar
2016-08-25 10:26:08 cri
Hukumar kula da yanayi da albarkatun ruwa ta kasar Myanmar, ta sanar a jiya Laraba cewa, an samu aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 bisa ma'aunin Richter a tsakiyar kasar Myanmar. Girgizar kasar dai ta auku ne da misalin karfe 5 da minti 4 na yamma.

Rahotanni sun nuna cewa wurin da girgizar kasar ta fi karfi na da nisan kusan kilomita 197.9 daga kudu maso yammacin tashar hasashen girgizar kasa ta birnin Mandalay. Kaza lika zurfin girgizar kasar da ta auku ya kai kilomita 84.1 a karkashin kasa.

An ji girgizar kasar a birnin Nay Pyi Taw, da jihar Mandalay, da jihar Yangon da wasu sauran wuraren dake kasar. Wasu mazaunan yankin Pagan-Nyaung U, da masu yawon shakatawa a wurin sun bayyana cewa, annobar ta lalata wasu mashahuran wurare, da hasumiyoyin ibada dake wurin. Kana ta lalata wani bangare na ginin majalissar kabilun dake birnin Nay Pyi Taw. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China