in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa a Ecuador ya karu zuwa 272
2016-04-18 15:24:53 cri
Bisa sabbin alkaluman da gwamnatin Ecuador ta bayar, an ce, yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 272 sakamakon abkuwar girgizar kasa a yankin dake kusa da teku dake arewa maso yammacin kasar. Yanzu ana aikin ceto cikin gaggawa.

Shugaban kasar Ecuador, Rafael Correa Delgado ya bayyana cewa, lardin Manabi na fama da bala'i mai tsanani, yayin da yankin Pedernales ya riga ya lalace, wanda ke a tsakiyar bala'in. Shugaba Rafael Correa Delgado ya furta cewa, abin dake gaban kome shi ne ceton mutane daga buraguzan gine-gine a yanzu.

A wannan rana kuma, mataimakin shugaban kasar, Jorge Glas ya isa yankin dake fama da bala'in domin ba da jagoranci, inda ya yi kira ga duk jama'ar kasar da su hada kansu a cikin wannan mawuyacin halin.

Kawo yanzu, gwamnatin Ecuador ta tura sojoji dubu 10, da 'yan sanda da masu kashewa gobara 4600 zuwa lardunan da suka fi fama da girgizar kasa. Haka kuma ma'aikatar sufuri da ta kiwon lafiya sun dauki matakan gaggawa, na jigilar kayayyakin ceto zuwa wadannan yankuna.

Game da wannan batu, jakadan Sin a kasar Ecuador ya furta cewa, har zuwa yanzu babu rahoton da aka bayar dangane da mutuwa ko jikkatar mutanen Sin sakamakon wannan bala'i a birnin Quito, hedkwatar kasar, amma ana ci gaba da kokarin samun tabbaci dangane da ko akwai mutanen Sin da suka mutu ko jin rauni a yankunan dake kusa da tekun.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China