Black Starlets dai ta kwashi kashin ta a hannu, bayan da Burkina Faso ta dura mata kwallaye 4 da daya. Sai dai duk da hakan, tsiran maki daya dake tsakanin kungiyoyin biyu bisa jimillar wasannin da suka buga a baya, ya baiwa Ghanan damar buga wasa na gaba da Cote d'Ivoire a wannan zagaye.
A baya dai Black Starlets ta Ghana ta dauki kofin wannan gasa har karo biyu, a wannan karo ma 'yan wasan ta na ci gaba da kokarin samun gurbin gasar, bayan da aka dakatar da kasar bisa sanya 'yan wasa da shekarun su suka haura 17 a gasar da ta gabata.
Ghana da Madagascar da sauran kungiyoyin kasashe 6 ne za su buga gasar ta shekarar 2017 a kasar Madagascar, wadda za a fara wasannin karshe na share fagen ta daga ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.