in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwallon kafar kasar Ghana ta dauki karin matakan tsaro a filayen wasa
2014-05-14 16:34:09 cri
Hukumar gudanarwar kwallon kafar kasar Ghana (GFA), ta sanar da daukar karin matakan tsaro a daukacin filayen wasan kasar, a daidai wannan lokaci da kasar ke cika shekaru 13, da aukuwar wani yamutsi ne shekarar 2001, wanda yayi sanadiyyar mutuwar 'yan kallo126.

A ranar 9 ga watan Mayun shekarar ta 2001 ne dai wani yamutsi ya auku, yayin da ake tsaka da wasa tsakanin manyan kulaflikan kasar biyu, wato Accra Hearts of Oak, da kulaf din Asante Kotoko na birnin Kumasi.

Cikin wata sanarwa ta jimamin tunawa da wannan rana, shugaban hukumar ta GFA Kwesi Nyantakyi, ya ce tuna wannan lamari tamkar matashiyace ga tashi tsaye, wajen ganin an dauki matakan kandagarki. Nyantakyi wanda mamba ne a hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ya ce tun daga wancan lokaci hukumar sa ta zage damtse, wajen ganin an kaucewa aukuwar wani lamari makamancin hakan a gaba.

"Bisa matakan fadada bincike, da kwararan manufofin hukunta masu karya dokokin wasa, hukumar GFA ta aiwatar da kudurorin wanzar da tsaro yayin gudanar wasanni". a kalaman Mr. Nyantakyi.

Kaza lika shugaban hukumar ta GFA ya ce duk da matakan da aka riga aka dauka aikin da ake yi bai kare ba. Domin a cewar sa za a kara kaimin aiwatar da manufofin gano manyan matsaloli daka iya bijirowa yayin wasanni, tare da daukar matakan wayar da kan 'yan kallo game da dokokin dake da alaka da hakan.

Bugu da kari Mr. Nyantakyi ya ce GFA ba zata manta da wadanda suka rasu sakamakon waccan balahira ba, za kuma ta karrama su ta hanyar daukar karin matakan kare aukuwar hadurra yayin gudanar da daukacin wasanin da hukumar ke lura da su a kasar ta Ghana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China