in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta daga a teburin FIFA na kulaflikan kwallon kafa mafiya iya taka leda
2014-08-20 16:55:07 cri
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce kasar Ghana, ta daga daga matsayin da take a baya da daraja 2, a teburin kulaflikan duniya mafiya kwarewa wajen buga tamaula.

Sabon teburin da FIFAr ta fitar ya nuna cewa, a yanzu haka Ghana ta daga zuwa matsayi na 36 daga na 38. Inda ta samu maki 648, sama da 642 da take da shi a watan Yulin da ya gabata, ita ce kuma ke takewa Czech Republic baya a matsayin duniya a jadawali na biyu, da hukumar ta fitar bayan kammalar gasar cin kofin duniya na Brazil.

A nahiyar Afirka kuwa kungiyar kasar ta Ghana ce ke matsayi na 4, inda a can sama kuwa Aljeriya ke matsayi na 1, sai Kwadebuwa ta 2, ya yin da kuma Najeriya ke a matsayi na 3.

Hukumar ta FIFA ta kuma ce Jamus ce ke ci gaba da rike matsayin ta na daya a duniya, sai kuma Argentina a matsayi na 2, ya yin da kuma Netherlands ke ci gaba da kasancewa a matsayi na 3.

Abubuwan da FIFA ta yi la'akari da su wajen fidda wannan sakamako sun hada da manyan wasannin kasa da kasa 23 da kulaflikan suka buga, da suka hada da wasannin sada zumunta 10, da kuma wasannin share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka 13.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China