in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ba ta da nufin karya dokokin FIFA, in ji ministan wasanni
2014-08-07 19:54:13 cri

Ministan ma'aikatar kula da wasanni da harkokin matasa na kasar Ghana, Mahama Ayariga, ya kaddamar da wani kwamitin bincike a ranar Litinin, domin duba dalilan da suka janyo gazawar kulaf din kasar, ya yin wasannin da ya buga a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Brazil.

Ya yin gasar ta cin kofin duniyar dai kungiyar Black Stars din ta kammala wasannin ta uku ne da maki daya tak, bayan karawar da ta yi da Amurka, da Jamus, da Portugal, aka kuma fitar da ita a zagayen gasar na farko.

Sai dai a cewar minista Ayariga, ba wai an kafa wannan kwamiti ne domin cin zarafin wani ba ne, ba kuma a nufin karya dokokin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ba. A cewar sa an kafa kwamitin ne kawai domin gano hakikanin abin da ya faru, ta yadda jama'ar kasar za su samu damar sanin dalilin da ya sa burinsu game da kulaf din ya gaza cika.

Haka kuma a cewar Ayariga, sakamakon binciken da kwamitin zai gudanar, zai baiwa kasar damar gudanar da shawarwari, da sauye-sauye, wadanda za su bada damar inganta tsarin wasannin kwallon kafa da ma samar da ci gaba ga kulaf din na Black Stars ya yin wasannin da zai fuskanta a nan gaba.

Ministan ya kara da jaddada manufar aikin wannan kwamiti, yana mai bayyanawa hadaddiyar hukumar kwallon kafan kasar GFA, da hukumar FIFA cewa, ba za a karya wata doka da hukumar FIFA ta gindaya ba. Kaza lika ya bukaci GFA da ta aike da wasika ga hukumar FIFA domin karin bayani game da hakan.

Kwamitin dai mai kunshe da mutane 3, dake karkashin jagorancin alkalin wata kotun daukaka kara mai sun Senyo Dzamefe, zai yi binciken yadda ta kasance ya yin da kungiyar kasar ta Ghana ke gudanar da shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniyar da ta shude, tare da gano matsalolin da suka hana kungiyar taka rawar gani ya yin gasar da ta gudana a Brazil.

Har wa yau kuma, kwamitin zai gudanar da bincike kan yadda aka kula da magoya bayan kungiyar kasar wadanda suka halarci gasar ta duniya ta kasar Brazil domin goyon bayan kungiyar ta su, da sauran batutuwan da suka shafi moriyar jama'a mai alaka da kungiyar ta Black star a waccan gasa.

Bugu da kari kwamitin zai kwashe kwanaki 30 ya na gudanar da aikin sa, sa'an nan ya mika rahoton binciken da ya gudanar ga ministan matasa da wasannin kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China