in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shahararriyar 'yar wasan gudun famfalaki ta kasar Kenya Cheruiyot ta samu tagomashi bayan samun lambar zinare a gudun mita 5,000 a Rio Olympic
2016-08-24 13:28:35 cri
Bayan samun nasarar da 'yar wasan gudun famfalakin ta kasar Kenya Vivian Cheruiyot ta yi a gudun mita dubu 5, ana sa ran zata taka rawar gani a wasannin Newcastle a wata mai zuwa.

'Yar wasan mai shekaru 34 a duniya, ta isa birnin Nairobi tun a jiya Litinin, kuma an tabbatar da cewar yanzu burinta ya cika, na samun daukaka a wasannin gudun famfalaki. Kuma ta sha alwashi halartar wasannin da za su gudana a Newcastle a wata mai zuwa.

'Yar wasan ta fada a Nairobi cewa; " na jima ina yin wannan mafarkin, kuma kowa yana sane da irin shirin da nake yi na samun wannan babban matsayi".

Cheruiyot, wacce ta kasance fitattaciyar 'yar wasan tseren mita 10,000, wannan shine karo na uku da take shiga wasannin Olympics, a wannan karon kasar Kenya ta samu nasarar lashe lambar zinare 6, da azurfa 6, da kuma tagulla 1 a wasannin na Rio. Cheruiyot ta bada gudunmowa ga cimma nasarar ne bayan da ta ci lambar zinare a tseren mita 5,000, da kuma azurfa a tseren mita 10,000.

A bisa tarihin wasannin Cheruiyot, wannan shine karo na 4 data halarci wasannin Olympics, ragowar sune na Sydney a 2000, da Beijing a 2008 da kuma London a 2012.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China