in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasannin duniya ta sanya wa jami'in Kenya takunkumi
2016-02-25 08:26:39 cri
Humumar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya IAAF, ta kakabawa wani babban jami'in hukumar wasannin kasar Kenya Isaac Mwangi takunkumi, na hana shi gudanar da ayyukan da suka shafi wasanni cikin tsawon kwanaki 180, yayin da kuma za a gudanar da bincike kan zargin da ake yi masa na cin hanci da rashawa.

Wannan matakin da hukumar IAAF ta dauka ya sanya Mwangi, zama babban jami'in hukumar AK ta kasar Kenya na 4, da aka dakatar daga aiki sa, bayan shugaban hukumar AK Isaiah Kiplagat, da mataimakin shugaban David Okeyo, gami da jami'in hukumar mai kula da kudi Joseph Kinyua, wadanda dukkansu aka dakatar da su daga aiki a watan Nuwambar da ya gabata.

A makon da ya gabata ne dai, wasu 'yan wasan gudu 2 dake karkashin takunkumin, wato Francesca Koki Manunga, da Joy Sakari Nakumincha, suka kai karar Mwangi, cewa ya bukace su da su ba shi cin hanci na kudi da ya kai dalar Amurka 24,000, ta yadda zai saukaka musu takunkumin da aka sanya musu, sakamakon yin amfani da magani mai sa kuzari lokacin da suke halartar gasar IAAF ta shekarar 2015, wadda ta gudana a birnin Beijing na kasar Sin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China