An dai tashi wasan da kungiyoyin biyu suka buga 2 da 1, a birnin Nairobin kasar Kenya.
A nata bangare kasar Guinea Bissau, ita ma ta doke Zambia da ci 3 da 2 a wasan da suka buga ranar Asabar. Yanzu dai Guinea Bissau ce ke kan gaba a rukunin ta, yayin da ya rage wasa daya ta kammala wasannin na share fage. Kafin wannan nasara ba a yi tsammanin Guinea Bissau za ta cimma nasarar samun gurbi a gasar dake tafe a badi ba. Sai dai nasarar da kungiyar ta samu a wasan ta na farko da Kenya, da kuma kunnen doki da Congo da Zambia suka buga har sau bi-biyu a wasannin su na baya sun sanya Guinea Bissau shigewa gaba a rukunin.
Da yake bayyana farin cikin samun wannan nasara, kocin Kenya Stanley Okumbi, wanda ya maye gurbin Bobby Williamson a watan Fabarairu, ya ce nasarar da suka samu ba tashi ba ce shi kadai, nasara ce ta 'yan wasa, da 'yan kasar Kenya baki daya. Ya ce ya tabbatar kowa na farin ciki da wannan nasara. Duk da kuma babu isasshen lokaci na gina kungiya mai karfi, amma nasarar da suka samu kan Congo ta kayatar da kowa. (Saminu Alhassan)