in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Kenya sun iso birnin Beijing gabanin bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ajin kwararru ta duniya
2015-08-19 16:04:44 cri
Gabanin bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ajin kwararru ta duniya da za a bude a ranar 22 ga watan Agustar nan a nan birnin Beijing, tawagar 'yan wasan kasar Kenya ta iso birnin Beijing, tare da burin ta na kafa tarihi a gasar ta wannan karo.

Wannan dai gasa na kasancewa abun alfaharin kungiyoyin kasashen duniya, kasancewar ta na kunshe da manyan 'yan wasa kwararru daga sassan duniya daban daban.

A wannan karo tawagar kasar Kenya na kunshe da mutane 68, da suka hada da 'yan wasa 54 da za su fafata neman lambobin bajimta a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da za a kwashe mako daya ana gudanarwa.

Rahotanni sun nuna cewa tawagar ta baro 'yan wasanta uku, wato Edna Kiplagat, da Visiline Jepkesho da kuma Helah Kirop, wadanda ake sa ran za su iso Beijing a ranar 24 ga watan nan.

A cewar shugaban tawagar kasar ta Kenya Joseph Kinyua, suna da imanin kara yawan lambobin yabo da suka samu a baya, musamman a gasar birnin Moscow inda Kenyan ta zo ta 4 da lambobin yabo 12, wato Zinari 5, da Azurfa 4 da kuma Tagulla 3.

Kinyua ya kara da cewa, sun zabi 'yan wasa mafiya hazaka, domin cimma burin da suka sanya gaba, duk da hakan ya ce kasar Sin ba za ta zamo kanwar lasa ba, haka ma Jamaica da Amurka wadanda suka yi fice a wannan gasa a baya.

Bugu da kari, Kinyua ya yi hasashen cewa gasar ta birnin Beijing za ta zamo mafi girma cikin makamantan ta 15 da suka gabata, tun fara gudanar ta a shekarar 1983.

Shi ma a nasa tsokaci babban kocin 'yan wasan na Kenya Julius Kirwa, cewa yayi 'yan wasan sa za su baje basirar su a gasar ta wannan karo, duba da cewa sun samu horon da ya dace, wanda zai basu damar fuskantar kalubalen dake gaban su. Ya ce tawagar ta wannan karo na kunshe da 'yan wasa ajin farko da ka iya mamaye gasar.

A gasar birnin Moscow da ta gabata, kasashe da yankuna 203 ne suka halarta, a kuma wannan karo, gasar birnin Bejing na fatan karbar sassan 'yan wasa 1936, wadanda suka hada da maza 1043 da kuma mata 893.

Bisa tarihi kasahen Rasha, da Amurka da Jamaica ne ke kan gaba a wannan gasa da yawan lambobin yabo.

Rasha dake matsayin farko, na da jimillar lambobi 17, wato Zinari 7 da Azurfa 4 da Tagulla 6. Sai Amurka dake da lambobin yabo 25, wato Zinari 6, da Azurfa 13, da kuma Tagulla 6. Yayin da Jamaica ke da jimillar lambobin yabo 9, wato Zinari 6, da Azurfa 2 da Tagulla 2.

Cikin tawagar 'yan wasan na Kenya na wannan karo, 6 daga cikin su sun halarci gasar Olympics ta birnin Beijing wadda ta gudana a shekarar 2008. Cikin su kuwa hadda Asbel Kiprop, dan tseren gudun mita 1,500, da Ezekiel Kemboi da Brimin Kipruto, 'yan tseren mita 3,000 na gudu da tsallake shingaye. Sai kuma Viola Kibiwott, da Janeth Jepkosgei 'yan tseren mita 800, da kuma Edwin Soi, dan tseren mita 5,000. Duka wadannan 'yan wasa ana sa ran sake ganin su a filin "shekar tsuntsu" dake nan birnin Beijing a gasar duniya ta wata mai zuwa.

Kenya dai ta dade tana taka rawar gani a fagen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Ga misali 'yar wasan kasar Vivian Cheruiyot, ta taba lashe tseren mita 10,000 a gasar birnin Daegu na Koriya ta Kudu a shekara ta 2011, a kuma wannan karo za ta sake gwada sa'ar ta a wannan aji, bayan ta tsallake gasar 2013 wadda ba ta halarta ba, sakamakon haihuwa da ta yi a lokacin. Za kuma ta fuskanci abokiyar karawar ta 'yar kasar Habasha Gelete Burka, wadda ta lashe tseren mita 1500 a gasar champion ta shekarar 2008.

Har wa yau a bana Kenya za ta gabatar da Julius Yego a gasar birnin Beijing. Wannan dan wasa na taka rawar gani ne a wasan Javelin, kuma ya zamo zakaran nahiyar Afirka a wannan wasa. A wannan karo Yego wanda ya zo na 4 a gasar birnin Moscow, na fatan kafa tarihi a gasar birnin Beijing dake tafe.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China