in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tseren Kenya sun yi nasara a gasar gudun yada kanin wani Belgrade karo na 29
2016-04-22 08:54:32 cri
'Yan tseren Kenya Abel Rop Kipruto, da Stellah Barsosio, sun yi nasara a gasar gudun yada kanin wani ta Belgrade fadar mulkin kasar Serbia, wadda ta gudana a ranar Asabar kuma ta kasance karo na 29.

Kipruto ya lashe gudun da aka fafata ne ajin maza cikin sa'o'i 2 da mintuna 23 da dakika 59, yayin da ita kuma Stellah Barsosio, ta lashe tseren na ta bayan ta kammala a sa'o'i 2:43:41.

Bayan kammala gasar Kipruto ya ce ya ji jiki matuka, kasancewar akwai zafi, inda ma'aunin zafi a ranar ya kai degrees Celsius 25, amma duk da haka ya yi matukar gamsuwa da sakamakon da ya samu. Ya ce wannan ne karo na biyu da ya halarci gasar gudun yada kanin wani ta Belgrade, kuma sakamakon da ya samu mafi sauri shi ne sa'oi 2 da mintuna 16.

A na ta bangare Stellah, wadda wannan ne karon farko da ta halarci wannan gasa ta Belgrade, cewa ta yi nasarar da ta samu ta faranta ran ta matuka, musamman ma ganin irin kalubale da 'yan tseren suka fuskanta a yayin gudun.

Da yake tsokaci game da tsarin gudanar gasar, Daraktan ta Dejan Nikolic, ya ce ya gamsu da salon yadda ta gudana, kasancewar a wannan karo gasar ta samu karin kaso 33 bisa dari na yawan mahalartan ta, kana da karin kaso 50 bisa dari na baki 'yan kasashen waje da suka shige ta.

Ya ce a gasar rabi, da kuma cikakken zango na gudun yada kanin wani, an samu 'yan tsere 6,000 daga kasashen duniya 60. Tare da kuma masu sha'awar shiga tseren don nishadi su 20,000.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China