Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin, Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin tana nuna rashin amincewarta da duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci, kuma tana yin Allah wadai da hare-haren boma-bomai da suka faru a wuraren da ke gabar tekun da ke arewa maso yammacin kasar Syria a kwanan baya wadanda suka haddasa mutuwar dimbin fararen hula tare da jikkatar wasu.
Rahotanni na cewa, a ranar Litinin 23 ga wata ne, aka kai wasu hare-haren kunar bakin wake a biranen Jableh da Tartus da ke gabar teku a arewa maso yammacin kasar ta Syria, wadanda suka halaka mutane a kalla 148, kana da dama suka ji raunuka.(Lubabatu)