A karshen zagaye na uku na ganawar da suka yi jiya Lahadi a birnin Khartoum na kasar Sudan, wakilan kasashen Sin da Norway, Amurka da kungiyar tarayyar Turai sun bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna da su samar da yanayin da ya dace don a gudanar da bincike kan tashe-tashen hankula na baya-bayan da suka barke a kasar, ta yadda za a gudanar da cikakken bincken da zai ga hukunta duk wanda aka samu da hannun wajen keta yarjejeniyar tsagaita bude da aka cimma.
An kuma bayar da wata sanarwa a karshen ganawar, wadda ta jadadda muhimmancin daukar matakan da suka dace na magance tabarbacewar yanayin harkokin jin kai a Sudan ta kudu da kuma hana gurguncewar tattalin arzikin jajiriyar sakar. (Ibrahim)