Tawagar ta UNMISS ta ce ta damu matuka da barkewar fada tsakanin sassan biyu a yankin na Equatoria da wasu yankunan Sudan ta kudun,ciki har da Nassir da ke yankin Upper Nile.
Kakakin MDD Farhan Haq wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai, ya kuma ce ana ci da fuskantar zaman zullumi a Juba, babban birnin kasar.
Tawagar ta MDD dai ta yi kira ga dukkan bangarorin da ba sa ga maciji da juna da su mayar da wukakensu cikin kube kana su kyale masu kai kayan agajin jin su isa yankunan da ke matukar bukatar taimako.
Har ila tawagar ta UNMISS ta ce, ana samun rahotanni cewa, wasu sojoji sanye da kayan sarki da wasu kungiyoyin dakaru masu dauke da makamai da ba a tantance ba suna aikata laifuffuikan cin zarafi, wadanda suka hada da yiwa mata da kananan yara fgyade, tun lokacin da aka shiga zaman dar-dar a 'yan makonnin da suka gabata.(Ibrahim)