Mataimakin ministan watsa labarun kasar Sudan ta Kudu, Paul Akol, ya bayyana a birnin Juba a yayin wata hira a ranar Alhamis cewa kasarsa za ta tura a ranar Jumma'a da wata tawagar manyan jami'ai a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na farko, mista Taban Deng Gai, da aka nada ba da jimawa ba a wannan taro na Addis Abeba.
"Mun samu takardar gayyata domin halarta a wannan taron musammun na IGAD kan batun Sudan ta Kudu, amma kuma za mu tabo maganar tura sojojin kasashen waje, da ba za mu amincewa ba domin yarjejeniyar zaman lafiya tana nan daram", in ji Akol.
IGAD na kunshe da kasashen Afrika guda takwas wadanda suka hada da Djibouti, Erythrea, Habasha, Kenya, Uganda, Somaliya, Sudan da Sudan ta Kudu.
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar za su yi wani taro a ranar Jumma'a a Addis Abeba, domin wani zaman taron gaggawa kan rikicin Sudan ta Kudu.
Wannan taro ya biyo bayan sake barkewar tashe tashen hankali a ranar 8 zuwa 11 ga watan Yuli tsakanin dakarun 'yan tawayen rundunar sojojin 'yantar da Sudan dake cikin adawa (APLS-OI), dake karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na farko da aka sallama, Riek Machar, da sojojin dake biyayya ga shugaba Salva Kiir, rikicin da ya daidaita yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a cikin watan Augustan shekarar 2015 bayan ficewar mista Machar tare da dakarunsa daga birnin Juba.
Mista Deng ya maye gurbin shugaban 'yan tawayen cikin wani yanayin takkadama da rudani, a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa. (Maman Ada)