Wata Kungiya mai rajin kare kasar ta Sudan ta Kudu, wadda tsohon sakatare janar na hadadiyyar kungiyar neman 'yancin Sudan ta Kudu (SPLM) ke shugabanta, Mista Pagan Amum, na kokowar ganin cewar kasar ta kasance a karkashin wakilcin MDD.
A daya bangaren kuma Mataimakin Kakakin gwamnatin kasar Mista Paul Akol Kordit, ya tabbatar da cewa, Al'ummar Sudan ta Kudu ba zasu amince da gwamnatin hadin gwiwa karkashin kungiyoyin wajen kasar ba. Mista Amum wanda ya ke gudun hijira yana shugabantar wata kungiyar tsoffin yan gwagwarmaya wanda aka taba tsare mambobin ta bisa zargin cin amanar kasa, sa'an nan aka sake su sanadiyar barkewar tashin hankali a kasar a watan disamba 2013.
Wasu daga cikin mambobin kungiyar dai sun samu matsayi a cikin gwamnatin rikon kwaryar. Sai dai Mr. Amum ya kaurace wa gwamnatin rikon kwaryar kasar, inda yake rayuwa yanzu a kasar Amurka. Mista Akol ya ce lokaci yayi da za a kawo karshen tashe-tashen hankula a Kasar.
A baya dai Tsohon mashawarci shugaban Kasar Amarika Barack Obama, kuma tsohon jakada a Kasar Sudan da Sudan ta Kudu Mista Princeton Lyman, shi ne ya bada shawarar kasancewar kasar Sudan ta Kudu a karkashin wakilcin MDD ko AU. Ra'ayin dai na nufin tallafawa kasar har ta samu ikon tafiyar da mulkin kan ta bayan kawo karshen rabuwar kawuna a cikinta. Mista Lyman ya bada shawarar cewar, kasar ta kasance karkashin wakilci tsawon shekaru 10 zuwa 15. Tun tuni magabatan Juba sun yin Allah wadai da tura dakarun tarayya Afrika zuwa kasar.
Kungiyoyin kasar biyu dai sun jefa kasar cikin yakin basasa tun watan disamba 2013, har zuwa yarjejeniyar zaman lafiya mai tangal-tangal ta shekarar da ta gabata. (Laouali Souleymane)