in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar majalisar dunkin duniya ta yi tir da alawadai da cin zarafin fararen hula da ma'aikatan agaji a kasar Sudan ta kudu
2016-08-04 14:41:43 cri
Babban jami'i mai kula da ayyukan jin kai na MDD Mista Stephen O'Brien ya kaddamar da wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a ranar laraba da ta gabata a kasar Sudan ta Kudu, inda yayi kira na musamman zuwa ga bangarori biyu na kasar masu gaba da juna da su tabbatar da kare hakkin fararen hula da ma'aikatan agaji bayan tashe tashen hankalin da suka barke a cikin kasar, wadanda suka yi sanadiyyar janyo 'yan gudun hijira da dama a wurare masu yawan gaske a cikin kasar. Mista Stehen O' Brien yake cewa "al' ummar Sudan ta Kudu sun sha wahala sosai a tsawon lokaci''. Inda ya kara da cewa, ya yi bakin ciki sosai game da cin zarafi, da hare haren da sojoji kasar suke kaiwa fararen hula, game da wannan dayen aiki ne kuma, yayi kira da kawo karshen tashe tashen hankali cikin gaggawa tare kuma da gurfanar masu laifi gaban kotu. A cewar hukumar kula da harkokin agaji ta MDD (OCHA), cin zarafin fararen hula, da lalata kayayyakin agaji yana cigaba kamar yadda aka barnata ma 'ajiyar kayan abinci bayan hare haren da aka kai a birnin Juba.

Mista O'Brien ya bayyana cewa, tun cikin watan Disamba na shekarar 2013, a kalla ma'aikatan agaji 57 suka rasa rayukansu a kasar Sudan ta Kudu, inda daya daga cikinsu ya mutu a lokacin rikicin baya baya nan a Juba. Kuma har yanzu wasu da dama daga cikinsu ba a da labarinsu.

Duk da kalubale yau da kullum da suke fuskanta, ma'aikatan agaji musamman ma kungiyoyi masu zaman kansu wanda suke filin daga, suna namijin kokari domin kai taimako zuwa ga al'ummar dake cikin bukata.

Jami'in ya nuna matukar adawa da duk wasu hare hare kan mai'aikatan jin kai, tare da yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su dauki matakan musamman, domim kare ma'aikatan agaji ta yadda zasu samu zarafin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, da kuma kai taimako zuwa ga mutanen da ke cikin bukatun abinci da sauransu. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China