in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hedkwatar tsaron Najeriya ta karyata canjin da aka samu a shugabancin kungiyar Boko Haram
2016-08-05 09:31:03 cri
A jiya ne hedkwatar tsaron Najeriya ta karyata rahotanin da wasu kafofin watsa labarai suke yayatawa game da nadin sabon shugaban kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron kasar Rabe Abubakar ya rabawa manema labarai, ta bayyana cewa, canjin shugabancin kungiyar ta Boko Haram ba zai yi wani tasiri ga matakan da sojojin kasar suke dauka da nufin kakkabe gyauro 'yan ta'addan a yankin arewa maso gabashin kasar ba.

A ranar Laraba ne dai kungiyar ta Boko Haram ta sanar da nadin Abu Musab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar dake yammacin Afirka domin maye gurbin Abubakar Shekau. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China