in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton MDD: Tattalin arzikin duniya ba zai karu sosai ba
2016-05-13 11:22:07 cri
Bisa gyararren rahoton kyautata tattalin arzikin duniya na shekarar 2016 da M.D.D. ta fidda a ranar 12 ga wata, an ce, ana ci gaba da samun tafiyar hawainiyar farfado da tattalin arzikin duniya, kuma an yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 2.4 cikin 100 a shekarar 2016, kana zai karu da kashi 2.8 cikin 100 a shekarar 2017.

A yayin taron bayar da rahoto da kwamitin kula da tattalin arziki da zamantakewar al'umma na M.D.D. ya yi a wannan rana, an ce, tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 2.4 cikin 100, abun da ya yi kasa da kashi 0.5 cikin 100 bisa hasashen da aka yi a watan Disambar bara. Bisa rahoton, yadda ake rashin bukatun sayayya a kasashe masu wadatar tattalin arziki zai ci gaba da kawo matsala ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.

Rahoton ya ce, an yi hasashen cewa, kasashe marasa wadata za su samu saurin bunkasuwar tattalin arziki da yawansa ya kai kashi 4.8 cikin 100 a bana, kuma wannan adadi zai kai kashi 5.5 cikin 100 a badi, abun da ya yi kasa da kashi 7 cikin 100 da aka tanada a cikin shirin samun bunkasuwa mai dorewa. Hakika kasashe masu tasowa da wasu yankuna marasa ci gaban tattalin arziki suna fama da matsalar tafiyar hawainiyar GDP sosai. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China