in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria ta yi suka kan rahoton tsaro da Amurka ta fitar
2016-08-12 11:35:03 cri

Jiya Alhamis 11 ga wata, Nigeria ta sanar da cewa ana samun zaman lafiya a ko wace jiha a kasar, sakamakon da ya sabawa rahoton tsaro da Amurka ta bayar.

Ministan watsa labarai da al'adu na Nijeria Mista Lai Mohammed ya fadi haka ne yayin da karbi wata tawagar masu aikin yawon shakatawa ta kasar a birnin Abuja.

Amurka ta bayar da wannan rahoto ne wanda jaridun kasar da dama suka wallafa shi, Mohammed kuma ya musanta abubuwan da aka rubuta a cikin rahoto, cewa wai babu zaman lafiya a jihohin 20 a Nijeria, sun zama wurare masu hadarin gaske. Ministan ya yi gargadi wasu jaridu da su kaucewa wallafa irin wadannan rahotoni, saboda za su rage kwarin gwiwar masu zuba jari da masu yawon shakawara daga kasashen waje.

Ban da wannan kuma, ministan ya yi kira ga kafofin yada labaru da kuma mambobin kungiyar mai kula da harkokin yawon shakawata da su ba da taimako ga gwamnati don kyautata sha'anin yawon shakawata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China