Shugaba Xi ya yi wannan kiran ne cikin wani sakon taya murna da ya aikawa dandalin hadin gwiwar kafofin watsa labarai game da shirin Ziri daya da hanya daya na wannan shekara da aka bude yau Talata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A cikin sakon, shugaba Xi ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen gina hanyar siliki maras gurbata muhalli cikin lumana wadda za ta amfana al'ummomin da shirin ziri daya da hanya ya ratsa ta cikinsu.
Taron wanda jaridar people daily ta kasar Sin ta shirya, ya samu halartar wakilan kafofin watsa labarai 212 daga kasashe 101.(Ibrahim)