Firaministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi a bikin bude taron ministoci ne na kasashen sashen gabashi da yammacin Afirka game da yaki da hamada karo na 5 da ya gudana a Dakar na kasar Senegal.
A cewarsa, matsalar tsaron tana haifar da karuwar ayyukan ta'addanci, lamarin da ke shafar galibin kasashen da ke yankin na Sahel.(Ibrahim)