Sanarwar ta ce, an gudanar da tattaunawar siyasa kan rikicin Burundi a ranar 21 zuwa 24 ga wata, mai shiga tsakani na kungiyar EAC, kuma tsohon shugaban kasar Tanzania Benjamin Mkapa ne ya shugabanci tattaunawar. Mkapa ya ce, za a kira bangarorin Burundi da ba su halarci tattaunawar ba don su shiga tattaunawa ta sabon zagaye, game da haka kuma Ban Ki-Moon ya nuna yabo sosai kan matakin.
Baya ga haka, Ban Ki-Moon a cikin sanarwar ya jaddada cewa, idan ana son warware rikicin siyasar Burundi, dole ne a gudanar da tattaunawa bisa tushen kundin tsarin mulkin Burundi, kuma bisa yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da zaman jituwa na Burundin. Ban Ki-Moon ya bayyana goyon baya ga kokarin da ake yi wajen warware rikicin Burundi ta hanyar lumana, ya kuma bayyana cewa, MDD na fatan taka rawa a kai.
Tun daga watan Aflilun shekarar 2015, sakamakon rashin jin dadi da jama'ar kasar suka nuna ma jam'iyya mai rike da ragamar mulki wadda ta nuna goyon baya ga shugaba Pierre Nkurunziza da ya yi tazarce kan shugabanci, kasar Burundi ta fada cikin tashen tashen hankali da zanga-zanga. (Bilkisu)