A saboda haka, wannan mataki na gwamnati, ministar kiwon kifi da halittun ruwa ta kasar Sherry Ayittey ta yi kira ga masuntan kasar da su hanzarta yin rajista domin amfana da wannan dama yadda ya kamata, domin magance kalubalolin da za su iya fuskanta sakamakon hadarurrukan da ke faruwa ba zato ba tsammani.
Bisa wannan shirin inshora, masunta za su sami kudi idan kayayyakin aikinsu suka lalata sakamakon hadarurruka, ko kuma idan wani ya rasu a yayin da ya ke gudanar da ayyukan da abin ya shafa ko kuma ya ji rauni har ba zai iya yin wannan sana'a ba.
Haka kuma, ko da ba su gamu da hadari ba, a karshe masunta za su sami kudin inshora da gwamnatin ta biya musu tun farko. (Maryam)