in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi alkwarin tallafawa kasar Ghana wajen ci gaban aikin gona
2016-06-30 11:41:25 cri
Gwamnatin kasar Sin ta jaddada aniyyarta na tallafawa kasar Ghana wajen raya ci gaban aikin gona da samar da ababen more rayuwa gami da ci gaban fasaha.

A yayin bude dandalin tattalin arzikin Sin da Ghana a ranar Talata, jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ta fada cewar abinci shi ne abu mafi muhimmanci ga ci gaban kowace kasa a duniya.

Ta ce abinci shi ne abu na farko da dan adam ke bukata a rayuwa. Kuma aikin gona shi ne hanyar samar da abinci da tufafi domin rayuwar jama'a, kuma su ne tushen ci gaban masana'antu da bunkasuwar tattalin arziki.

A cewarta a kasar Sin, gwamnati a ko da yaushe tana ba da fifiko mai yawa wajen bunkasa aikin gona, kuma ta kafa wasu muhimman bangarori hudu da suka hada da ci gaban masana'antu, da sadarwa, da raya birane, da kuma aikin gona irin na zamani, domin samar da ingantaciyar al'umma mai matsakaicin ci gaba daga dukkan fannoni.

Jakadar ta ce sassan hudu dukkanninsu na taimakawa juna, idan har babu bangaren noma na zamani wanda tushen da masan'antu ke bukata, daga nan sai a samu bayanai da raya birane, a cewarta idan babu wannan fanni tamkar bishiya ce da ba ta da saiwa.

Sun, ta bayyana samar da hukumar inganta filayen noma wato SADA a matsayin wani batu mafi muhimmanci da zai samar da ci gaba ga kasar ta Ghana.

Hukumar ta SADA ta samar da kadada miliyan 8 wanda zai dace da noma don samar da kudaden shiga da samar da ma'adanai irin su zinare, da kuma samar da makamashi marar illa ga muhalli.

A karkashin wannan dandali na Sin da Ghana, gwamnati kasar Sin ta yi alkawarin karfafawa kamfanoninta gwiwa domin samar da hukumar ta SADA, wanda za ta taimaka wajen daga darajar ci gaban harkokin kasuwanci da tattalin arziki ga wannan dandali na kasashen biyu.

An kafa hukumar SADA ne da nufin cike gibin dake tsakanin yankunan kudancin Ghana da arewaci da kuma gabashi da yammacin Volta da yankunan Brong-Ahafo.

An kafa dandalin ne da nufin inganta ci gaban SADA domin karfafa ci gaban hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu domin samun sakamako mai armashi.

Mataimakin ministan kasuwanci da masana'antu na kasar Ghana Ibrahim Murtala Muhammad, ya yabawa taimakon da kasar Sin ke baiwa Ghana shekaru masu yawa da suka gabata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China