Bikin na tsawon kwanaki uku ya samu halartar wakilai daga La Brea na Trinidad da Tobago.
Ministar yawon bude ido da raya al'adun kasar Ghana, Elisabeth Ofosu-Agyare ta nuna farin ciki kasancewar wannan shi ne karo na uku da aka gudanar da bikin a zamaninta, kuma bikin ya samu magoya baya daga ciki da wajen kasar.
Ta ce bisa irin nasarar da aka cimma tana fatar a nan gaba bangaren yawon bude ido zai samu bunkasuwa ta yadda zai kasance babban hanyar musaya tsakanin kasar da kasashen waje.
An nuna bajinta iri dabam dabam a lokacin bikin daga dukkan shiyyoyi 10 na kasar wanda aka gudanar a wani gari dake daura da babban birnin kasar.
Ministar ta kara cewa, yadda bikin ya samu halartar mutane masu yawa ciki har da dalibai daga dukkan fadin kasar, hakan wata alama ce dake nuna bikin yana samun karbuwa a kasar da ma kasashen duniya ta yadda a nan gaba kasar za ta dinga samun kudaden shiga daga wannan fanni. (Ahmad Fagam)