in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Ghana sun sha alwashin aiwatar da zabe cikin lumana a kasar
2016-06-11 12:56:31 cri
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya lashi takobin tabbatar da kwanciyar hankali a babban zaben kasar dake tafe a watan Nuwambar wannan shekara

Mahama ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin tunawa da kafuwar jam'iyya mai mulkin kasar shekaru 24 da suka gabata, ya ce jamiyyar ta NDC ba zata taba shiga duk wani lamari da ya shafi tada hankula ko cin zarafi ko yin batanci a lokacin gangamin yakin neman zabenta ba.

Shugaban na Ghana ya bukaci dukkannin jam'iyyun siyasar kasar wadanda zasu shiga zaben na bana dasu dauki dukkan matakan tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China