Rundunar sojin Najeriya ta ce, dakarunta dake aikin tabbatar da tsaro a yankunan jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 16, sannan sun kwato makamai da dama.
Mai Magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Sani Usman, ya fada cikin wata sanarwar da ta iske kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin cewa, mayakan na Boko Haram sun yi yunkurin kaddamar da hari ne a yankin Kangarwa dake jahar, da misalin karfe 5 da rabi na yammacin ranar Lahadi, sai dai dakarun Najeriya sun dakile harin, sannan sun fatattaki mayakan.
Usman ya ce, makaman da sojin Najeriyar suka kwato, sun hada da wasu makaman roket 7, da wata na'urar harba bam guda, da bindigogi samfurin AK-47 guda 11, da motar daukar manyan bingigogi, da wasu manyan bindigogi masu sarrafa kansu da wayoyin hannu da dai sauransu.
A cewarsa, wani babban soja guda da kuma kananan sojoji 11 sun samu raunuka a lokacin bata kashin.
Mai Magana da yawun dakarun na Najeriya ya ce, sojojin za su ci gaba da aikin sintiri a yankunan ba kakkautawa.(Ahmad)