in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar UNESCO ta isa Najeriya domin karfafa dangantaka
2016-08-11 09:53:43 cri

Daraktar janar ta hukumar ci gaban ilmi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO Irina Bokova, ta isa Najeriya a jiya Laraba 10 ga wata, inda ta fara ziyarar aiki, a kokarin karfafa dangantaka a tsakanin hukumarta da kasar wacce ke yammacin Afrika.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, ziyarar madam Bokova, wani bangare ne na ziyarar aiki da hukumar ta UNESCO ke gudanarwa a kasashen yammacin Afrika da Afrika ta Tsakiya, domin tallafawa kasashen na Afrika wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali karkashin shirin neman ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030.

Madam Bokova za ta gana da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar, domin tattauna yadda za'a karfafa ci gaban ilmi, da al'adu, da kimiyya, da aikin sadarwa, da kuma yada labaru, da kuma yadda za'a magance matsalar tashe-tashen hankula da tsattsauran ra'ayi.

Wata sanarwa wadda ofishin yada labarai na MDD ya fitar ta bayyana cewar, ziyarar ta UNESCO za ta tabo muhimman batutuwa da suka shafi manyan ajandodin kungiyar tarayyar Afrika AU na shirin shekarar 2063.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China