Asusun kula da yawan al'umma na MDD UNFPA ya ce, a kalla mutane miliyan 1 da dubu 100 dake zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a jihohin Borno da Yobe da Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya na fama da matsalar karanci cibiyoyin kiwon lafiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta UNFPA dake Najeriya Habib Kori ta fitar wanda ta iske kamfanin dillancin labarun Xinhua ta ce, mazauna sansanonin na cikin matsananciyar bukatar cibiyoyin kula da lafiyar mata, da cibiyoyin kula da kwakwalwa da tunani.
Sanarwar ta kara da cewar asibitocin na wadannan jihohin na fuskantar matsaloli na karancin ma'aikata da rashin kayayyakin aiki wanda zai cimma muradun al'ummomin dake yankunan.
Mai magana da yawun hukumar ta bayyana cewar, kayayyakin da ake da su na aikin jin kai na kiwon lafiya a shekarar nan ta 2016, zai iya isar mutane miliyan 2 da dubu 600 ne kadai daga cikin mutane miliyan 3 da dubu 700 dake cikin matsananciyar bukatar kula da lafiyarsu.
Kori ta kara da cewar, kashi 30 cikin 100 na mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar ko kuma yankunan dake karbar bakuncin 'yan gudun hijirar, ba su da damar samun muhimmiyar kulawar kiwon lafiya.
Ta ce, shirin ba da agaji na UNFPA ya tallafawa asibitoci sama da 120 da kuma kebe wasu cibiyoyi 9 na kula da mata da 'yaya mata tsakanin shekarar 2015 zuwa watan Yulin 2016, inda kusan mutane dubu 960 suka amfana.(Ahmad Fagam)