A jiya Asabar gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar ta cafke biyu daga cikin fitattun 'yayan kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers (NDA) a birnin Warri na jihar Delta dake kudancin kasar.
Kwamandan rundunar sojin ruwan kasar Joseph Dzunye, ya fada a taron manema labarai cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ne jami'an sojin suka damke tsagerun a yankin Sapele dake jihar Delta.
Dzunye ya ce, 'yayan kungiyar ta NDA da aka kama su ne Felix Miyenminiya mai shekaru 53, da kuma Stanley Jongha, mai shekaru 35, mutanen biyu su ne kanwa uwar game wajen daukar nauyin kaddamar da hare hare kan kamfanin hakar mai na Chevron tsakanin watan Mayu zuwa watan Yulin wannan shekara.
Jami'in sojin ya kara da cewa, mutanen suna da hannu dumu dumu wajen farfasa bututun mai da kuma yin fashi a teku.
Ya ce rundunar sojin ruwan Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron kasar sun sha alwashin murkushe batagarin wadanda ke lalata kayayyakin aikin hako man kasar a yankin na Niger Delta mai arzikin mai.
Dzunye ya ce rundunar sojin ruwan ba za ta kyale batagarin su durkusar da tattalin arzikin kasar ba.
Kungiyar tsagerun ta NDA ta sha yayata aniyarta na cigaba da kaddamar da hare hare kan bututan man fetur da iskar gas na kasar dake yankin mai arzikin man.
Hare haren ya haifar da koma baya ga sha'anin tattalin arzikin Najeriyar a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar komawar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya wanda shi ne babbar hanyar samun kudaden shigar kasar.(Ahmad Fagam)