Gwamnatin Najeriya ta gargadi 'yan canji a kasar, da su kaurace wa cin ribar da ta haura kaso 2 bisa dari, kan kudaden kasashen waje da za a rika ba su daga babban bankin kasar. A daya hannun kuma, gwamnatin ta ce, bankunan da za su rika samar wa 'yan canjin kudade, ba za su ba da abin da ya haura dalar Amurka 30,000 ga ko wane dan canji a mako guda ba.
Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta, babban bankin na Najeriya CBN ya ce, 'yan canjin na da damar zabar bankunan da za su rika karbar kudaden waje daga gare su a duk mako.
CBN ya bayyana cewa, 'yan canjin za su rika sayen kudaden wajen kan farashin da ba zai haura karin kaso daya da rabi ba, sama da farashin sauran cibiyoyin musayar kudi na kasa da kasa. Kaza lika sanarwar ta ce, kudaden da 'yan canjin za su rika karba, za su sayar da su ne ga masu bukatar kudaden tafiye-tafiye ciki hadda 'yan kasuwa, da masu biyan kudin makaranta, da masu zuwa jiyya kasashen ketare.
Har wa yau sanarwar ta ja kunnen 'yan canjin da su kaurace wa karya wadannan sharudda, domin kaucewa fushin hukuma. (Saminu)