Yaki da Boko Haram: An bukaci al'ummomin dake kan iyakoki dasu bada hadin kai mai kyau
Rundunar hadin gwiwa (FMM) dake kunshe da sojojin Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru, domin yaki da kungiyar Boko Haram, ta yi kira ga al'ummomin dake rayuwa a kan iyakokin wadannan kasashe da su ba da hadin kai mai kyau ga jami'an tsaro, in ji wata sanarwar FMM da aka fitar a ranar Talata a birnin Niamey. Domin baiwa jami'an tsaro damar zakulo mayakan kungiyar kishin islama na Boko Haram da suka warwatsu a cikin wannan yanki, komandan FMM, janar Lamidi Adeosun ya yi kira ga al'ummomin kwarai dake kan wadannan iyakoki, masu neman ganin tsaro ya tabbata, da su rika sanar da jami'an tsaro ga duk wani zuwan gungun duk wasu mutane baki a yankinsu. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku