in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta damkawa kasar Sudan ragamar gudanarwar sararin samaniyar ta
2016-08-14 13:08:41 cri
Sudan ta kudu ta yanke shawarar sallamawa makwabciyarta Sudan ikon gudanarwar sararin samaniyarta, bayan da damar gudanar da shi ta kubuce mata a sakamakon yaki da ya daidaita kasar.

Ministan yada labaran kasar Sudan ta Kudu Michael Makuei, ya bayyana cewar, a halin yanzu kasar ba za ta iya gudanar da al'amurran hukumar kula da zirga zirgar jirage a sararin samaniyar kasar ba, sakamakon tashe tashen hankula da kasar ke fuskanta.

Makuei, ya fadawa 'yan jaridu cewa, Sudan ta Kudu ta amince ta damkawa gwamnatin Sudan al'amurran da suka shafi gudanarwar zirga zirga ta sararin samaniyar kasar, abin da kawai take bukata shi ne, kasar Sudan ta dinga sanar da ita halin da ake ciki game da batun a lokaci zuwa lokaci.

A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta balle daga kasar Sudan a matsayin kasa mai cin gashin kanta, bayan kada kuri'ar raba gardama, bayan shafe sama da shekaru 20 ana fuskantar yakin basasa. Tun daga lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta, gwamnatin Sudan ce ke cigaba da gudanar da iko game da sararin samaniyar Sudan ta Kudun.

Sai dai masu nazari kan al'amurra na dora alamar tambaya game da matakin da gwamnatin Sudan ta Kudun ta dauka na mika ragamar harkokin sararin samaniyarta ga tsohuwar uwar gijiyar tata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China