in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Gai a matsayin mataimakin shugaban Sudan ta kudu na farko
2016-07-27 09:57:11 cri

A jiya Talata aka rantsar da Taban Deng Gai a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko a Sudan ta kudu a gwamnatin hadin kan kasa.

An rantsar da Gai ne bayan sallamar Riek Machar daga mukaminsa a ranar Litinin, bayan yin watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu a watan Agustan 2015, lamarin da ke ci gaba da jefa jaririyar kasar cikin yakin basasa.

A ranar Lititin ne shugaban kasar Kirr ya nada Gai, wanda shi ne tsohon mai shiga tsakani na tsohuwar kungiyar dakarun kwatar 'yancin Sudan wato SPLM-IO, bayan da aka samu rarrabuwar kai tsakanin mambobin kungiyar 'yan tawayen a Juba, inda a ranar Asabar mambobin SPLM-IO suka gabatar da sunansa a matsayin wanda zai maye gurbin Machar, bayan da Machar din ya fice daga Juba, kwanaki kadan bayan barkewar sabon fada tsakanin dakarun dake biyayya ga shugaban kasar Kirr da na Machar.

A jawabinsa na kama aiki, Gai ya ce, zai yi amfani da wannan dama wajen cike gibin da Riek Machar ya bari, kuma zai tabbatar da daukar matakai da za su ceto yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a watan Agustan 2015.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China