in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu na cikin wani mummunan hali, in ji Ban Ki Moon
2016-07-29 10:46:54 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya bayyana matukar damuwa game da mummunan halin da Sudan ta Kudu ke ciki a halin yanzu, yana mai cewa abubuwan da suka auku a kasar a baya bayan nan, na nuna yadda aka yi hasarar muhimmiyar dama, ta wanzar da zaman lafiya da lumana tare da adalci a kasar.

Mr. Ban wanda ke wannan tsokaci, cikin jawabin sa na bude zaman mahawarar kwamitin tsaron MDD, ya ce ya kadu bisa jin irin tarin rahotanni dake nuni ga yadda ake keta hakkokin bil'adama, da aikata fyade ga fararen hula a kasar. Ban Ki Moon ya ce akwai bukatar gaggauta daukar matakan shari'a ga masu aikata irin wadannan laifuka, a hannu guda kuma wajibi ne shugabannin kasar su rungumi matakai na wanzar da zaman lafiya mai dorewa. Hakan a cewar sa batu ne da ke jan hankalin kowa.

A farkon wannan wata ne dai fada ya sake barkewa tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna a birnin Juba fadar mulkin kasar ta Sudan ta Kudu, lamarin da kuma ya sabbaba kisan mutane 272, ciki hadda fararen hula 33.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China