in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu da su ci gaba da tsagaita bude wuta
2016-07-27 11:37:24 cri

Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana jiya Talata, cewar game da matakin kawar da Riek Machar daga mukaminsa na mataimakin shugaban kasa na farko na Sudan ta Kudu, da shugaban kasar Salva Kiir ya dauka, MDD ta yi kira ga bangarori daban daban na kasar da su tabbatar da tsagaita bude wuta, da kuma warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari cikin lumana. Tawagar musamman ta MDD da ke kasar Sudan ta Kudu ma za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin hada kai na wucin gadi da kuma bangarori daban daban da abin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya.

Haka zakila, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana a ranar cewa, rikicin da ya auku a kasar Sudan ta Kudu a 'yan kwanakin nan ya riga ya tilastawa mutane a kalla dubu 37 sun yi gudun hijira zuwa kasar Uganda. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China