in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya yi marhaba da amincewar kasar Sudan ta Kudu domin tura sojojin kasa da kasa
2016-08-08 13:51:15 cri

Sakatare janar na MDD ya yi marhaba da amincewar Sudan ta Kudu da tura sojojin kasa da kasa domin kare al'ummar kasar daga tashe-tashen hankalin tsakanin bangarorin kasar masu gaba da juna. Sudan ta Kudu ta tsai da wannan kuduri ne a lokacin zaman taro na kasa da kasa wanda ya hada da kasashen da ke gabashin nahiyar Afirka. Mista Ban ki-Moon ya yi kira ga bangarorin kasar masu gaba da juna wajen kawo karshen tashe-tashen hankalin cikin kasar domin aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a kasar. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China