Bisa al'ada, kamata ya yi bangarori daban daban su daina kowane irin yaki dake tsakaninsu daga kwanaki 7 kafin kaddamar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi a karo na 31 zuwa kwanaki 7 bayan gasar wasannin Olympics na nakasassu na yanayin zafi a karo na 15.
Ranar 29 ga wata, rana ce ta kwanaki 7 kafin kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Rio, shi ya sa Ban Ki-moon ya yi kira da cewa, koda yake a daina tsagaita bude wuta sosai a duniya, amma tunanin Olympics na bukatar da a kawar da wahalhalu. Ya yi kira da a yi kokari kamar yadda ake neman samun lambobin yabo a yayin wasanni, domin cimma burin daina yake yake a duk fadin duniya a lokacin. Wannan zai bayyana ra'ayin gasar Olympics, wato girmamawa, da sada zumunci, da hadin kai, da kuma adalci.
Ban Ki-moon ya bayyana cewa, an kafa kungiyar 'yan wasa masu gudun hijira a wannan karo, hakan ya bayar musu zarafi na samun lambar kyauta. Wannan ya bayyana karfin 'yan gudun hijira, tare da bayyana wa duniya cewa, dole ne a kara kokarin daidaita matsalar 'yan gudun hijira, inda rikice-rikice suka zama dalilan wannan matsala. Shi ya sa bin tunanin Olympics na daina yake yake zai bayyana ra'ayin hadin kan kowa da kowa, in ji mista Ban.(Fatima)