A yayin ziyararsa, mista Wang ya gana da shugabanni da kuma takwarorinsa na kasashen uku, tare da jinjinawa 'yan kasarsa dake wadannan kasashe dake taimakawa al'ummomin wuraren wajen yaki da cutar Ebola, musammun ma manyan likitoci da sauran ma'aikatan kiwon lafiya.
Ya shaida wa 'yan jarida a kasar Guinea, zangonsa na karshe, cewa Laberiya ta bayyana kawo karshen cutar Ebola, kuma ya yi tsammanin cewa kasashen Saliyo da Guinea su ma za su iya cimma wannan burin nan da dan lokaci mai zuwa.
Muhimmin matakin hana sake barkewar annobar wannan cuta shi ne na kawar da talauci da kuma bullo da wasu hanyoyin kusantar cigaba mai karko, in ji mista Wang.
A cikin wannan shirin, kasar Sin za ta kasance wani abokin hulda mafi nagarta na nahiyar Afrika, in ji mista Wang.
A cewar Wang Yi, matsalar halin da muhimman ababen more rayuwa ke ciki da kuma rashin ma'aikata na kasancewa muhimman kalubaloli ga cigaban tattalin arziki da na al'umma na wadannan kasashen uku, kuma kasar Sin a shirye take ta samar musu da tallafi a ko da yaushe.
Ya tabo maganar masana'antu, tsarin kiwon lafiya da kuma tsaron abinci a matsayin muhimman fannonin da kasar Sin a shirye take wajen bada taimako.
A Saliyo, mista Wang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta taimakawa kasar wajen kafa wata cibiyar ba da kulawa da yin bincike kan cututtukan dake adabar wannan shiyya.
Kasashen uku da cutar Ebola ta daidaita sun nuna godiyarsu ga kasar Sin game taimakon da ta bayar wajen yaki da cutar, kuma sun dauki niyyar kara karfafa huldar dangantaka tare da kasar Sin.
Shugaban Saliyo, Ernest Bai Koroma, ya bayyana cewa amsar gaggawa da kasar Sin ta bayar da kuma taimakon da ta bayar a zahiri sun taka mihimmiyar rawa wajen yaki da annobar Ebola a kasarsa. (Maman Ada)