in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya ya ce kasar za ta koyi Sin wajen bunkasuwar tattalin arziki
2015-12-08 10:25:24 cri
Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu, ya ce, gwamnatin kasarsa za ta koyi dabarun da kasar Sin ke yin amfani da su har ta samu bunkasuwa ta fuskar tattalin arziki, ta yadda kasar za ta iya dogaro da kanta, da kuma kaucewa dogaro da kudaden tallafin da kasashen duniya ke baiwa kananan kasashe.

Shugaban ya furta hakan ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin din nan bayan komawa kasarsa daga halartar dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika wato FOCAC, ya ce, yana da matukar muhimmanci ga kasar ta yi karatun ta nutsu wajen nazarin irin hanyoyin da kasar Sin ta yi amfani da su har ta samu matsayin kasar dake kan gaba a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki.

Jaridar Zambiya Daily Mail ta rawaito Edgar na cewa, kasar Zambiya ta ga tasirin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, ya kara da cewar, kasarsa ba za ta lamunci dogaro kan kudaden tallafin kasashen duniya ba.

Ya ce, ko da a rayuwa irin ta bil Adama, daraja da kima na tare da wanda ya dogara da kansa, ya ce dole ne Zambiya ta koyi darasi daga kasar Sin, irin jajurcewar da kasar Sin ta yi a shekarun baya dubi yadda ta zama a yau, akwai darussa da dama da za'a koya kan hakan.

A cewar Edgar, ya zama wajibi ga sauran kasashen Afrika su zage damtse, domin dogaro da kan su, kasancewar 'yancin kowace kasa ya ta'allaka ne da yadda ta ke iya cin gashin kanta ta fuskar tattalin arziki.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China