in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zambiya zai rattaba hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar
2015-12-16 10:30:36 cri
Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu, ya ce a shirye yake ya rattaba hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da zarar ya isa ofishin sa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne majalisar dokokin kasar Zambiyan ta amince da aiwatar da kudurin doka na shekarar 2015, wanda ya bada damar yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar, bayan samun kiraye kiraye daga al'ummomin kasar na mika bukata ga 'yan majalisar dokokin kasar dasu amince a yi wa dokokin kasar kwaskwarima.

To sai dai Lungu, ya shedawa manema labaru kafin ya tashi zuwa arewacin kasar don duba wasu muhimman ayyukan da suka shafi ci gaban al'ummar kasar, cewar wasu mutane sun bukace shi don ya magance sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin cikin hanzari.

Ya ce, a shirye yake ya rattaba hannu kan dokokin da zarar sun isa ofishin sa, kamar yadda al'ummar kasar suka jima suna son aiwatar da hakan, sai dai ya ce, abin bakin ciki ne ganin yadda wasu mutane ke kin amincewa da duk wani matakin ci gaba da gwamnatin kasar ke son dauka.(Ahmad Inuwa)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China