Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya ba da wannan tabbaci jiya Talata a Abuja,babban birnin Najeriya, a lokacin da ya ke jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban kasar Benin Patrice Talon wanda ya ke ziyara a kasar.
Shugaba Buhari ya ce, Najeriya tana duba yiwuwar saukaka yadda za a yi jigilar iskar gas din zuwa kasashen da ke yankin yammacin Afirka. Ya kuma godewa Jamhuriyar Benin bisa ga goyon bayan da ta ke baiwa Najeriya a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
A nasa jawabin Shugaba Talon ya ce, kasar Benin za ta farfado da dangantakar da ke tsakaninn kasashen biyu, musamman a fannonin cinikayya,da tattalin arziki,da bunkasa makamashi da kuma harkar Ilimi.
Sai dai kuma shugaba Talon ya bayyana damuwa game da karuwar ayyukan fasa kwauri a kan iyakokin kasashen biyu. A don haka ya jaddada bukatar ganin an magance wannan matsala ta yadda kasashen za su kara samun kudaden shiga.(Ibrahim)